Tun tasowar ta bata san dad'in rayuwa ba, ta taso cikin rayuwar tsangwama, kyara da hantara, a lokacin da take tsaka da gwagwarmayar rayuwa k'addara mai girma ta afka mata wacce ta k'ara jefa rayuwarta a rud'ani da kyamatar al'umma, Ta rasa gata, ta rasa dukkan farin ciki, yayin da ta fad'a zazzafar k'aunar mutumin da bai san tana yi ba, mutumin da yafi k'arfinta ya mata nisa na har abada, wanda hakan ya sake jefa ta a mayunwancin hali....All Rights Reserved