Qaddarar zuciya; a rayuwa za ka iya son wani a yayin da shi kuma bai da buqatarka, hakan kuma ba yana nufin ya tsaneka bane, dalili kuwa shi SO mai duka ne ke Éarsawa a zuÆatan bayinsa, babu wanda ya isa ya saka wa wani son wani ba tare da ubangiji ya rubuta hakan ba. So kan komawa ta zamto kiyayya a inda kiyayya ke koma wa ta zamto soyayya, shi yasa ma Manzon Allah ya ce " kaso masoyinka kaÉan kaÉan don watarana zai iya dawowa maÆiyinka, sa'annan ya ci gaba da cewa ka Æi maÆiyinka kaÉan don watarana zai iya zamto masoyinka"
Labarin dake tattare da tausayi, ban takaici, maida alkairi da sharri, son maso wani, kiyayya, nadama, tsantsan talauci, arziki, biyayya, sadaukarwa. Duk a cikin wannan littafin mai suna AKASIN ZUCIYA!
Makaho ne shi, baya gani ya samu wannan lalurar ne tun haihuwarsa. Da zuciyarsa yake ganin komai, Allah yayi masa muguwar fasaha da basira. Talakawa ne su sosai wannan dalilin ya Sanya iyayensa kasa sama masa lafiyar idanunsa.
Tun ganin sa da tayi zuciyarta ta kamu da tsananin kaunarsa, ta taimakesa ta kasance da shi, itace kawai ke masa san so, ita ce kawai ta nuna masa so da kauna duk da kasance warsa makaho (nakasaishe).
Tana taimaka masa amasa aiki a idanuwansa har ya soma gani, tun budewar idanuwansa ya ji duk duniya babu Wanda ya tsana sama da ita. Amma yana kunyar maida alkairi da sharri. Shin ya zai tunkareta da batun nan? Shin ya kyautata mata kuwa?. Just relax and find out in this hilarious story where haterate turns to love, love turns to pure haterate find out in AKASIN ZUCIYOYI BIYU
Shin Ya zata kaya tsakanin waanan bayin Allah biyu? Zai SO ta? Ko zai ki ta?.
Ku biyoni don jin yadda zata kaya.