SAMRA tafi ganema kayan aro da ƙarya domin da ita take famtamawa ta shiga duk inda nake son shiga, tahanyar yin ƙarya ita ɗin ɗiyar masu hannu da shunice, har ta taimaki na ƙasa da ita duk da cewa ita ɗinma ba kowa bace face ƴar aikin kakar wani atajiri mai kuɗi ƊAN MAMA, yayinda kakarta gwoggo ke ƙara ɗaure mata ƙugun yin ƙarya ganin cewa ta samo mai hali ta aura, agarin abuja dan itama ta huta ta shiga jirin matan manya, duk da cewa mahaifiyarta bata son halin da suke ita da gwoggo tana tsawata mata, amma gwoggo na ƙara yimata tsaye, kwatsam ta haɗe da ɗan uwanta tallaka wanda Allah ya ɗaura mata sonsa dare ɗaya, yaya zatayi da kakarta dake burin ganin cewa ta auri atajiri.?