* ZUWA GA MASOYA *
* MASOYAN ZAMANI *
* A wannan zamani da muke ciki, mafi yawa daga cikin masoya sukan yiwa soyayya wata fassara ta musamman *
* Yaudara tayi yawa cikin rayuwar masoyan wannan zamani *
* Tun daga bangaren samari har ya Zuwa bangaren 'yan Mata, ko wanne da irin tasa gudun mawar warin samar da Yaudara a Cikin rayuwar masoya *
* Saboda haka masoya maganin wannan matsala ta Yaudara cikin rayuwar masoya itace: AJI TSORON ALLAH *
* KOGIN KALAMAN SOYAYYA*
* Masoyiyata: 'kaunata gareki ingantacciya ce, wacce babu Yaudara a Cikin ta *
* Masoyiyata: sanyin muryarki ne abu mafi sanyar da zuciyata *
* 'Kadangare kan samu shiga cikin bango idan har bangon ya tsage.*
*To hakama soyayya takan samu shiga cikin zuciya idan har ta samu mukullin wannan zuciyar *
* Farin cikina: Soyayyarka ta zame mini tamkar inuwar jikina, duk wani motsi da zanyi to nakanyine tare da ita *
* Bana tunanin rayuwa zata iya gudana idan har babu ruwa da iska.*
*Haka Jin Dadi tare da walwala bazasu tabbata a gareni ba idan har bana tare da 'kaunarki *
* Kowacce rayuwa akwai abu mafi amfani a gareta.*
*Abu mafi amfani a rayuwata shine soyayyarka
*
* Gimbiyar Mata: Bana tunanin rayuwa zata iya aiwayar min da wani abu batare da soyayyarki ba