Tabbas ta fishi gaskiya a ko ina, ya za'ai su dinga abubuwa irin na ma'aurata bayan ba auranta zai ba, shak'uwarsu k'ara k'arfi take ta na gudun da basu san bigiren da za ta ajiyesu ba, ya na jinta a can k'asan zuciyarsa, itace farin cikinsa itace rayuwarsa, ita ta fara gina Katangar farin cikin da ya dad'e da rusheta a babin rayuwarsa, bai tab'a nuna rauninsa ga kowa ba sai akanta, itace zai shiga jikinta ya yi kuka kuma ta rarrasheshi ta sanya masa nutsuwa a zuciyarsa, to ta yaya zaiyi sakacin da zai rasata gaba d'aya?
Inama zai iya auranta da sai ya fi kowa farin ciki domin auranta shine burin zuciyarsa, ruhinsa da ma gangar jikinsa, amman hakan ba za ta tab'a samuwa ba bazai tab'a yafewa kansa ba idan har ya zamo silar mutuwarta, ya na hango tu'kuk'in bak'in cikin da zai d'and'ana na rashinta gaba d'aya Cikin Duniyarsa, abu d'ayane mafita a garesa dole ne ya nisanceta ya k'auracewa ganinta gaba d'aya amman kuma ta yaya hakan za ta kasance?
Bai tab'a jin bakin cikin abinda yai masa Katanga da aure ba sai yau, ya na jin inama zai iya rushe wannan Katangar ta yadda zasu gino sabuwar Katangar rayuwar auransu amman hakan ba za ta yuyu ba, hakan ya na da nasaba da rasata gaba d'aya cikin duniyarsa, kuma ya rasa da wani yare zai fahimtar da ita hakan.
Waye shi d'in wannan, kuma wace yake magana a kanta, kuma meye ya yi musu Katanga da auran da suke buk'ata?
Samun wannan amsoshin sai kun ninkaya cikin wannan littafi akan 300 kacal.
Rashuna Bebe'art ke muku fatan alkhairi.