Murya kasa kasa ya nemi sanin, "Feesah me ke damunki?"
Yayi shiru ko zata ce wani abu. Ko hada ido da shi taki yi.
"Kin tafi kin bar gari, kin kashe waya over a week, wannan hukuncin da kika yanke me kike so na fahimta kenan? Baki sanar da ni abinda nayi na bata miki ba, sai kika dauki mataki kamar kina kokarin cireni daga rayuwar ki? Me nayi miki haka?"
A nan ta kasa jurewa ta sa tafin hannunta biyu ta rufe fuskarta sai kuka mai karfi ya kwace mata, jikinta har jijjiga yake. Hankalinsa ya tashi ba kadan ba, yayi hanzarin matsawa daf da ita don ya bata baki amma ya kasa dora hannunsa jikinta domin hakan ya haramta gareshi.
"Haba Feesah wai yaya hakane? Gani gabanki ina tambayarki abinda ke damunki shine sai kuka kawai zakiyi kina fadar min da gaba. Idan ma laifi nayi miki na baki hakuri, ki fada min me nayi miki. Don Allah ki yi min magana."
Can dai ta dago fuskarta da ta tura cikin kujera ta fuskanci gabanta. Ganin haka yayi hanzarin saukowa daga kujerar ya danyi squatting a gabanta don ya iya kallon fuskarta. Ta ja gyale ta rufe fuskar, ya sa yatsa biyu ya janye gyalen.
Maganarsa tamkar rada, "My darling wanene yayi miki laifi?"
Shiru.
"Ni ne?"
Ta daga kai.
Ya ja gwaron numfashi, "Im so sorry ki yafe min. Menene laifin da nayi?"
Muryarta a shake, ga wasu sabbin hawaye masu dumi sun fara fita idonta tana magana a sanyaye, "Baka taba fada min akwai problem ba daga wajen mamanka. Dama tun farko shine reason din da yasa iyayenka suka ki zuwa gidanmu ka bari akayi min auren dole, har na fada mummunan yanayi, na sha wahala. Everytime sai dai kace min you love me baka taba fada min akwai any problem ba. Kuma last time a Yalleman I asked you kace ba zaka fada ba sai after munyi aure. Me yasa ka boye min?" Kasa cigaba da magana tayi don kukan ya kuma cin karfinta kawai ta ja mayafinta ta kuma rufe fuskarta.
"Kiyi hakuri sweetheart, anyi miki laifi. Amma ki sani ban boye miki ba don na cuce ki sai don ina gudun kada ya zamo sanadin da zamu bata."