15 parts Complete Saboda yadda mahaifin mu ya din ga saka Mana suna Fatima, har se da nayi tunanin ko Muna da alaka da shi'a ne, saboda Naga yawancin sune mutanen da ke saka Fatima sama da daya a gidajen su. Duk ma ba wannan ba, Shin kin taba Jin kunyar fitowa cikin mutane? kin taba Jin kunyar shiga taro? sau nawa like kallon Kan ki a madubi a Rana? to ni Ina kallon Kai na kamar sau ashirin a madubi, ba Wai Dan na duba kyan sura ta ba sede Dan na duba Naga ta Ina Zan fara daidaita hallitar jiki na, wasu suce min yeast, wasu suce min Fanke, wasu su Kira ni da Runduna, wasu su Kira ni da big Mamaa, wasu suce Fatibobom duk ni daya...
kunsan me ake Kira da Body Dysmorphic Disorder? kunsan irin illar da bakin ku take jawa mutane saboda yadda kuke kasa dauke idanu akan hallitar da ku da su Baku da say akai? kunsan yadda suke ji? kunsan irin kuncin da suke kwasa?
to ni shatuuu, kamar kullum na sake kawo muku sabon labari, akan sabuwar rayuwa, kamar kullum ba zakuyi Dana sani ba. ku zo kuji labarin BINTUN BATUUL