Safwan yace, " dama inasan ganin Nazir akwai muhimmiyar maganar dana zo da ita nake san mu tattauna " yana gama faɗa mahaifiyar su Nazir ta rushe da kuka sannan tace, " Nazir baya magana hasalima baya cikin hayyacinsa baisan waye ma akansa, kallan yayan Nazir tayi ta ce, " kai je kaxo mai da Nazir " nan take ya tashi ya fice sai gashi da wheel chair da Nazir aciki sai kallan mutane yake yana zubda hawu hannuwansa da ƙafafu gaba ɗaya sun shanye, Safwan na ganinsa cikin tashin hankali yace, " Wannan ne Nazir ɗin mai ya sameshi? " wani sabon kukan mahaifiyar su Nazir ta ƙara sawa, cikin ƙarfin hali yayan Nazir ya fara magana, " aranar da mahaifinmu ya rasu Nazir yace mana zaije gidansu Maryam, to bayan y dawo muna zaune sai gani mukayi ya zabura yana ihu yana cewa bazai kuma ba, sai kuma muka ga yana ta surutai daga haka kawai sai gani mukayi ya yanke jiki ya faɗi, shikenan har yau ka ganshi ahaka kullin magani ake bashi amma ba sauƙi kullin ciwon gaba yake yi. " gaba ɗaya jikin Safwan ne yayi sanyi cikin sumutar baki Safwan yace, " tabbas Marwan ne " karaf yayan Nazir yace, " wai waye Marwan ɗin nan naji lokacin da yake ta sumbatu yana cewa Marwan kayi haƙuri, ko kuma abokin aikinsu ne dan wannan ciwon ba tantama sihiri ne. " Safwan gaba ɗaya tausayi da tsoron halin da Nazir ke ciki ya kama shi.