Babu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta kasance. Daga ni sai ire-irena mu ke iya labarta yadda mace ta ke ji idan aka keta haddin yarta ko kuma ita kanta! Ina ma ace yau haddina ni Halimatu aka keta ba na yata ba?
GOBE NA...
Zawarcin Halimatu...
*** *** ***
Babu wanda zuciyarsa ta raya masa sai matar nan, sosai ya maida hankali yana kallon gurin da take zaune tare da yaranta, the way ta take sharar hawaye ya kara karafafa zatonsa a kanta, labarin yarsa ya shigo ciki duk kuwa da bata fadi sunansa ba ko sunan yarsa sai dai ta fadi cewar mahaifin yar ya zargeta da kisan yarsa saboda kaddarar mutuwarta ya fada mata, kamar yadda kadarar gushewar hankalin abokin aikinta ya fada a kanta, an keta mata haddi an ketawa yarta, mijinta ya ci zarafinta, a kokarin kwatar hakkin yarta mijinta ya saketa, ga labarin samun aikin kamfanin da tai ya shigo ciki sai dai shi ma bata fadi sunan kamfanin ba.....
Wani irin kallonta yake, har ya ji kamar gilashin dake idon sa ya tare ganinsa sai ta ya cireshi yana cigaba da kallonta, ita kuma ta soke kai kasa yana ta latsa waya tana sharar kwalla, wa akai wa fyade? Wacen karamar ko babbar? No wait mutunen da take bawa abincin a kusa da kamfaninsu abokin aikinta ne? Is that why take kokarin kula da shi? Waye mijin na ta? Waya ke bibiyarta?
A lokaci daya ya jerowa kansa wadannan tambayoyin, da bashi da amsar su, and he can't take his eyes on her kamar his life defend on her.
Tausayi da kuma taimako ya sa shi jajiɓota ya kawota cikin danginsa na Fulanin usul. Ta zauna cikin tsangwama da ƙyashi.
To kasancewarsu mabiya addini da kuma yare mabanbanta hakan bai hana soyayya mai sanyi ƙawalniya a zuciyarsu ba. Sai dai soyayyarsu ta zo da jarrabawa kala-kala. Wannan jarrabawa kuwa bai tsaya iya su ba, sai daya ya shafi 'yarsu Zaytoonah...
Cikin wannan tafiya zaku ga yadda ake SO da zuciya ɗaya. SO da baya tsufa. SO daya ke jure duk wani juyi-juyi na rayuwa.
SO ɗaya ne tak. Kuma Maryam Nkiru ta yiwa TJ shi. Duk rintsi, duk wuya soyayyarta na TJ ne.
Ku biyoni a labarin Chronicles of Zaytoonah dan samun labarin soyayya da kuma halin rayuwa...