53 parts Ongoing Na kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu ɗari bisa ɗari ba sai shi ɗin, ba zan kira hakan da jarabta, domin ko mahaifina bai sha ba akan yadda nake jin Mijina, bana ganin laifinsa sai nawa ina jin ban kyauta ba, na masa ƙwauron soyayya, rashin wadataccen abinci bai taɓa damuna ba, hatta ruɓewar da yarinyata tayi a ciki. ranar dana fahimci mara gurbi nake aure, matacciyya na zama, ina rayuwa cikin duhun kabarin da babu mai fiddani tambayar da zuciya ke mini me ya sanya ya zama MUNAFUKIN MIJI...