Yadda ya daga kai yana kallonta ne yasa ta shiga taitayinta babu shiri. Ya fara dumfararta gadan-gadan, kamar wanda yake shirin cinyeta danyarta. Duk dauriyarta kasawa tayi, ta fara ja da baya a rikice, idanunta sun fito waje kuru-kuru, dankwalin dake hannunta ta sanya tana kare fuskarta kamar shi zai kwaceta daga hannunshi.
Sai daya danganata da bango, ta jita ta lafe a jiki kamar zata shige ciki.,
Ya duka yana kallon tsakiyar idanunta da wani irin murmushi na gefen baki kwance akan fuskarshi, taji wasu abubuwa masu kama da jan wutar lantarki na yawo a sassan jikinta....
Murmushi ya sake saki, "kina ta babatu da daga murya akan Anty Ummynki Kauthar, sai dai, me yasa dana kalleki nake ji a jikina kamar ba ita kike tayawa kishi ba? Me yasa nake ji kamar.... kishina ne yake cinki? Me yasa nake hango tsabar kishina kwance a cikin idanunki, iye Kauthar? Me yasa??!!!".
Ganin yadda take faman zare idanu kamar kazar da aka lakume za a yanka, yasa ya ja da baya, wannan murmushi nashi dake matukar bata mata rai yana kara fadada akan fuskarshi, sai ya juya ya fita daga dakin. Ta sani, kamar yadda ya sani, bashi da sauran ta cewa, don kuwa ya riga ya gama daureta kam da jijiyoyin jikinta!
Ta silale a jikin bangon, zuciya na bugu kamar zata fasa kirjinta, ta samu kanta da maimaita tambayarshi a gareta, 'Me yasa? Kuma me yake nufi?!'.
*****************
***Zaku iya samun cikakken labarin a HIKAYA BAKANDAMIYA yanzu***
When jungkook awakened..he found in a novel world and had a become the villain, who was loathed by Male lead...
It's a novel story..and some of my thoughts
Taekook ff
Top tae
bottom kook
possesiveness
obsession
angst
other ships
twist
non-consent
Past story
Age gap
innocent koo
dominant tae
alpha × omega
Warning ⚠️
if ur not comfortable then don't read it