Duk yanda zan fasalta muku yanda take ta wuce nan, yarinya ce sangartacciya da iyayen ta suka ɓata ta da gata tun tana tsumman goyo, sun ɗau son duniya sun ɗaura mata, ba sa son kukan ta bare fushin ta, hakan yasaka ta taso babu kwaɓa take yin duk abin da taso.
yarinya ce me bala'in taurin kan tsiya, idan har tace zata yi abu, to, babu wanda ya isa ya hana ta, idan kuma tace baza ta yi ba babu wanda ya isa yasa ta tayi, ko kaɗan bata damu da rayuwan kowa ba, rayuwan ta kawai ta sani, duk wanda ya taka ta, to, tana ƙoƙarin ɗaukan mataki, bata da sabo ko kaɗan idan har ba da mahaifin ta ko Yayan ta ba.
ku biyo NI ku ji me zai faru da rayuwan ta, yarinya me tsatstsauran ra'ayi.
Zanen ƙaddaransa yana cikin zuciyarta, kamar yanda zanen nata ƙaddan ke cikin tasa zuciyar. Idan zuciyoyi suka haɗe waje guda akan samu wata irin zazzafan ƙauna. Ako da yaushe jinsa yake kamar wani baƙon halitta, RAUNI DAMUWA sune abun da sukayi tasiri wajen cika rayuwarsa, yasani kowani bawa da irin tasa ƙaddaran Amma shitasa Ƙaddaran takasance me girma ne agareshi....
***
hearttouching and destiny!!!