Cikin dare lokacin ƙafa duk ta ɗauke banda kukan tsuntsaye ba abunda yake tashi, alokacin ta farka daga bacci kayan wajen Goggo tasa ta ɗauko zumbulelen farin hijabin tasa, kwandon kayan kwalliyarta da shafe sati bata buɗeshi ba, ta buɗe ta ɗauko hoda ta zazzaga ta shafe fuskarta, hannu da ƙafafuwa Ludayin miyar Baba Huwaila da tun rana ta ɓoyeshi ta ɗauka ta sa a hijabi, ƴar fitilarta ta ɗauka ta fito daga ɗaki saɗaf-saɗaf ta je wajen bakin ƙofa ahankali ta zare sakata ta fice, kamar Aljana ita kaɗai ce a waje haka ta samu ta ƙarasa bayan katangar gidan Mai Gari ( _Dake gida huɗu ne tsakanin gidana Baba Huwaila da na Mai Gari_) ta kamata ta ɗane ta dirga.
A hankali ta ɗaga labulen ɗakin Mai Gari ta shiga ta same shi a kwance baccinsa yake hankali kwance, toshe bakinta tayi tana dariya ƙasa-ƙasa musamman da ta tuna irin muguntar da zata yiwa Mai Gari, sai da tayi ta gama ta koma saitin kan Mai Gari ta zaro ludayin miyar ta dai-dai ci kan sa ta bashi ƙwaaal, azabure Mai Gari ya tashi yana susar gurin baya yaja ganin mutum tsaye cikin fararen kaya.
Indo canja murya tayi shigen ta Goggo sannan ta fara magana, " Ni ce Goggo Kakar Indo Sarƙa nazo tafiya kai cen makwancina tunda cin Amana zakayi " Mai Gari cikinsa ne ya juya baiyi aune ba sai ji yayi ɗumi na bin wandonsa, Indo na ganin Fitsari na bin ƙafar Mai Gari ta gimtse Dariyarta ta kuma cewa.....🥱