Iska ce ta fara kaɗawa ahankali ta fara hango waɗansu irin manyan ƙwari masu kama a fasalin maguna sai dai kowanne su maƙale yake da fukafuki a gadon bayansa, sautin tafiyar Dokin ce ta ƙara kusantota hakan ne yasa ta maida kallonta ga inda tafi jin sautin na matsowa.
Kamar yanda ya bayyanar mata a karan farko wannan karan ma wata zabgegiyar Abaya ta hango baƙa, tsawon abayar ya kece tsawon bishiyoyin dake cikin dokar Dajin sai da ta ɗaga kanta sama sosai sannan ta hango dai-dai kansa sai dai kansa ne amma babu alamar fuska ajikinsa.
Ƙarasowa yayi gabanta ya tsugunna cikin murya mara daɗin sauraro ya fara magana, " Bingirsima baguar kinbasu wakisfatminar, kisasu biragu kilbasu tattarakimbas wajihagar, farafafus bintigad gurmanas YUSRA? harbaskila mindadu bar washbasbismas shizas kima bu warsa? " ( A karo na biyu ina ƙara miki barka da zuwa cikin daularmu nida ahalina, da sannu zan gabatar da ke ga sauran iyalaina domin kusan juna keda su ina fatan kina jina YUSRA? Ga ƴaƴana nan sun fara zuwa gaisheki ina fatan zaki basu kulawa ? ) Wannan zabgegen Aljanin ya ƙarasa maganar yana nuna mata waɗannan hallittun masu fasalin Maguna da fukafukai.
Yusra da tuni hawaye yake wankewa fuska ta ƙara durƙushewa ƙasa cikin sigar magiya tana faɗin, " Ka dubi girman Allah da Annabi ba dan ni ba, ba dan halina ba kayi haƙuri ka maidani cikin mutane dan Allah, wallahi bazan iya rayuwa cikinku ba na tuba dan Allah kamun rai "
Miƙewa tsaye yayi sannan yayi taku biyu zuwa uku sannan ya waigo ya ce mata, " Hargigas markusa bayas tinga " ( Tashi tsaye kije jikin waccen bishiyar kukar )
Yusra har tuntuɓe take da sauri ta miƙe tsaye saura kaɗan Abayar jikinta ta kayar da ita, jikin bishiyar taje ta tsaya tana sauraron abinda zai sake faɗa, batayi aune ba ta tsinkayi muryarsa yana faɗin.
" YUSRA Lilbas faragaras binsafa walgibas zalzulfat kinari " ( YUSRA kalli Abayar jikinki da kyau, idan har kin iya cireta daga jikinki