Shari'a saɓanin hankali. Barrister Aliyu wani gogagge kuma shaharren Barrister ne da tunda yake ba a taɓa yin nasara akansaba, baya karɓar shari'ar da ba gaskiya a cikinta ballantana yayi tunanin rashin nasara, kwatsam sai shari'a ta haɗashi da Barrister Zahra wacce ta kasance ɗaya daga cikin ɗalibansa, Zahra mace ce wacce ke da ƙoƙari wajen kwatarwa mai gaskiya hakkinsa, bata shiga shari'ar da babu gaskiya a cikinta sai dai wannan karon ta shiga ruɗani lokacin da ta fahimci Barristan da zasu gwabza a Kotu ba kowa ba ne illah Barrister Aliyu Haidar mai matakin SAN ɗaya daga cikin ƙwararrun Barristocin da ake kira da Senior Advocate of Nigeria ko ya wannan shari'a zata kasance?
NURA ISA S GARO