Ameera ta yi ajiyar zuciya gabanta yana dukan uku-uku domin zuciyarta ta fara raya mata abun da Ameer ya zo yi wajenta shi ya sa yake yi mata irin wannan kallon na bankwana wato Abubakar ya saye soyayyarsa kenan.
"Allah ya sanya alkairi"
Ta ce mishi cikin nuna ƙarfin hali domin kar ya gane halin ruɗu da damuwar da ta shiga. Ameer ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce,
"abu na biyu Ameera na zo ne muyi bankwana da juna domin bazan iya haɗa neman aure da Abubakar ba kasancewar ya fini komai kamar yadda ya lissafa"
Ameera ta girgiza kai cikin nuna takaicin abun da Ameer yake cewa sannan ta ce,
"bai fika komai ba Ameer, ko da ya fika to be kai ka a cikin zuciyata ba domin ni kai na ke so kuma iyayena sun bani damar na kawo musu wanda nake so kuma kai zan ce musu"
"bani ki ke so ba Ameera"
Ameer ya ce mata ta juya da sauri ta kalleshi ya gyaɗa mata kai sannan ya ci gaba da cewa,
"da ace ni ki ke so da ba wanda zai iya rabani da ke sai Allah. Na fahimci bani Ameer ɗin ki ke nema ba akasi aka samu wani ya baki lambata amman maganar gaskiya ni ba Marubuci ba ne ni ɗan kasuwa ne shagona yana kasuwar kwari shadda da atamfofin mata nake sayarwa. sunana na gaskiya Usman ana kirana da suna Ameer ne saboda sunan kakana aka samun dan haka Ameer wakilin sunana ne idan kuma kina sona a haka to zan aureki Ameera domin bana zaton yanzu a duniya akwai wanda zai ganki ya ce baya sonki sai dai kuma idan ya san baze samu ba musamman idan ya ji cewa matashin sojannan ne abokin takararshi to dole ya ja da baya..."
⚠BDSM
⚠dominance
Love in a dark heart
Sex can be intense, but we can't even imagine the love in that heart..🏳️🌈
〰️Please read this carefully〰️
⚠️️අතිශයින් වැඩිහියන්ට පමනක් වන මෙම කතාව මාගේ හිතලුවක් පමනක් බවට කාරුණිකව දැනු ම් දෙන අතර මෙම කතා මාලාවේ සියලුම චරිත මනක්කල්පිත බැවින් ඔවුන්ගේ සැබෑ ජීවිතයත් සමග කිසිම සම්බන්ධවයක් නැති බවට මෙයින් මා කියා සිටිමි.....
start - 2023.12.05