MASARAUTAR MU.. MASARAUTAR MU* SHIN KUN TAƁA JIN MASARAUTA MAI CIKE DA RUƊANI? SHIN KUNA SON KU SAN AL'ADUN NA CIKIN MASARAUTA? KUNA SON SUWAYE SUKE GADON SARAUTA? KUNA SON KUNJI YADDA KO WANNE MUTUM NA CIKIN GIDAN SARAUTA YAKE ƘWAƊAYIN KUJERAR MULKI?
Labarin *Masarautar mu* yana magana ne akan wani Masarauta wanda a shekarun baya yake cike da zalinci,daga baya kuma sai aka nada sabon sarki wanda yake cike da tausayawa talakawan sa,shi kuma sarkin d'an sa kwara d'aya ne kwal..........,shi kuma Yarima tun yana karami sarki ya fitar dashi zuwa 'kasar Turkish saboda farautar rayuwar shi da ake yi a cikin Masarautar,a inda yake zaune a can 'kasar kuma akwai Hibba wacce ta kasance babban 'ya a gun aminin sarki,babban burin mahaifiyar Hibba shine Yarima ya auri Hibba,ta yanda yaron Hibba zai kasance magajin Masarautar.
A Masarautar kuma akwai Iya wanda ya kasance 'kanin babanshi,babban burin Iya shi ne yarinyarsa Sulaymi ita ma ta auri Yarima,dan d'an da ta Haifa shi ma ya zama magajin Masarautar,a 'bangaren Masarautar kuma suma duk mu'karraban sarkin babban burin su suma shi ne su kashe Yarima,domin su amshi sarautar Masarautar.
Sai kuma ga Husnah,wacce ta dauke shi a matsayin yaya uwa d'aya uba d'aya,kwatsam kuma ba zato ba tsammani sai taji cewa shi ne mijinta,wad'an da ta d'auka a matsayin iyaye suka zama mari'kanta,wad'anda ta d'auka a matsayin yayyi wanda bata da kamar su,suka koma cousins d'in ta.