Yau sai ga Rayhana da Yaya Khalipha, bayan gushewar a kalla shekaru uku da doriya. Ta kasa hada ido da Yaya Khalipha wanda ke rungume da Asma'u a kirjinsa. Shima Ibrahim rungume da takwaransa, kowanne ya kasa ajiye dan ya yi tukin motar.
Dukkansu suna gaba, ita da Mimtaz suna baya. Jefi-jefi Rayhanah kan saci kallon Yaya Khalipha, ya yi kiba 'yar kadan ta hutu, ya kara murjewa. Da ganinshi za ka fahimci cikin kwanciyar hankalinsa yake, sannan likkafa ta yi gaba ko daga irin motar da ya dauko su a ciki da Balarabiyar da ya aje mai neman kashewa mutum ido don haske da hasken idanu.
Mimtaz ba ta da bakunta ko kadan, sai jan Rayhanah take da hira ta ji Hausa zau kamar (vedan) a dalilin rayuwa da su Jawahir, in ka ji tana Larabci to ita da iyayenta da danginta ne, amma ko Khalipha da Hausa suke magana.
Ta ce, "Yaya Khalipha aniyarka ta bika, ka ce 'yar Dr. Ibrahim da Rayhanah muni za ta yi, gata nan ta fi duk iyayen kyau da haske".
Ya ce, "Ai albarkacin sunan Mami ne shi yasa ta dan washe".
Ya kara duban yarinyar cike da kauna yana fadin,
"Lallai Muhd. Mansur ya yi mata, zuki!" Ya sumbaci 'yar.
Sai a lokacin ya juya ga Rayhana yana murmushi ya ce,
"Madam kinsha aiki, mun gode fah".
Tana murmushi ta ce,
"Aikin me Yaya Khalipha?"
Ya mikawa Mimtaz Asma'u ya tada motar ya ce,
"Aikin haifo mana UWA, ba ta barota a komai ba".
A ranta ta ce,
"Allah yasa kada ta yo halinta".