DIYAH Na tashi cikin gata da soyayya,ban rasa komi ba a rayuwata bangaren dukiya ko wani abu na kyale-kyalen rayuwa amma hakan baisa na kasance cikin farin ciki ba. Ada ina rayuwa cikin farinciki da soyayyar Ahali,cikin kankanen lokaci kaddara ta giftawa Rayuwata wacce ta yi sanadiyar rasa farin cikina. Mahaifina ba ya son talaka ,ba ya son ya rab'eshi idan ba lokacin bukatarsu ya yi ba wato lokacin zabe . A ya yin da ni kuma murmushi ya kan samu muhallin zama akan fuskata ne idan na kasance cikin talakawa, ina ganin yadda suke gudanar da rayuwarsu har nakanji ina sha'awar zama cikinsu domin sukan gusar da duk wata damuwata idan ina tare dasu. Narasa abu mafi muhimmaci a rayuwata sanadin wani tsatstsauran ra'ayi na mahaifina sannan na rabu da ahalina sanadin soyayyar talaka wacce tayi kutsen shigowa rayuwata ba tare da shirina ba. kubiyoni domin jin cikakken labarin HALIMATUS-SADIYAH [DIYAH]