NANA AMINATU 2022

NANA AMINATU 2022

  • WpView
    Membaca 18,065
  • WpVote
    Vote 927
  • WpPart
    Bab 56
WpMetadataReadDewasaLengkap Kam, Mei 12, 202211h 32m
Maganganun ta tamkar saukar kibiya take jin su a zuciyarta duk idan ta tuna, suna sukan ta su hana ta sukuni, suna tarwatsa ta su saka ta taji ita ƙasƙantanciya ce wacce bata kai ɗin ba kamar yadda take cewa, tana ganin baƙin kanta a koda yaushe a wacce bata kai ba, ko kaɗan bata taɓa saurara mata ba, ya za'a yi ta dena kallon kanta ta daban a cikin mutane yayinda take tuna duk wata kalma ta ɓatanci da take bin ta dasu a kullum ranan duniya? tun sanda ta buɗe idanuwanta da wayon ta take jin waɗannan munanan kalaman da ke tarwatsa mata duk wani farin ciki da jin daɗin ta. Sai dai kuma a duk sanda take jiyo kalaman sa sai ta ji ƙwarin gwiwa har ta kalli kanta a wacce ta kai kuma ta isa, ashe akwai ranan da zata yi farin ciki haka? Akwai ranan da wani zai iya yabon ta har ya nuna mata tana da matsayi fiye da sauran Mata? She can't believe that... Shi ne Mutum na farko da yake faɗa mata kalaman da idan ta ji su take ganin ta kai Mace, ta kai Mace cikakkiya ba wacce ta rako Mata ba, a kullum ganin kanta take yi a bata kai matsayin ba, ita bata kai Macen da zata iya fitowa ayi gwagwarmaya da ita a matsayin ta na ɗiya Mace ba. Shin wane ne shi wannan ɗin? Tabbas Ƙaddara kowa da irin tasa, wasu tana zuwar musu da sauƙi wasu kuwa akasin hakan, ba wai don wani ya fi wani bane a wurin Allah hakan ke faruwa, a'a, sai dai don Allah na gwada ko wanne bawa ta hanyar ɗaura masa tashi ƙaddaran, walau me sauƙi ko akasin sa, ko wanne bawa da tashi ƙaddaran kuma kowa yana fatan ace ya tsallake ƙaddaran da Allah ya ɗaura masa. Haka itama NAANA AMINATU tayi fafutuka a cikin rayuwar ta domin ta ga ta cinye nata ƙaddaran da ta kasance babba a gare ta. Na san Kuna so ku bibiyi labarin ta domin ku ji mene ne ya faru a rayuwar ta, to ku bi Ni sannu a hankali Zan warware muku komi a cikin sauƙi, ina fata labarin zai zame muku darasi a cikin rayuwa.
Seluruh Hak Cipta Dilindungi Undang-Undang
Bergabunglah dengan komunitas bercerita terbesarDapatkan rekomendasi cerita yang dipersonalisasi, simpan cerita favoritmu ke perpustakaan, dan berikan komentar serta vote untuk membangun komunitasmu.
Illustration

anda mungkin juga menyukai

  • 💤A MAFARKI NASANTA💤( I know her in my dream )
  • 🌸RAYUWAR MU A YAU🌸
  • MUNAFUKIN MIJI
  • KAICO NAH
  • GADAR ZARE
  • SAFEENATU
  • NAJWA Complete ✔
  • RUHI BIYI (a gangar jiki daya)
  • KUSKURE
  • NAUYIN BAKI

Haka take ta faman Lilo da k'afafun ta tare da sakin k'ayataccen murmushinta,tana cigaba da binsa da kyawawan idanunta masu haske kamar wata k'aramar yarinya cikin Rashin damuwa tana k'ara fad'ad'a murmushin ta Wanda ke nuna Babu abun da ke damunta ayanzu. A hankali Kuma murmushin Dake ke kwance akan kyakkyawar fuskar ta yafara gushewa inda ya koma b'ata fuska sai Kuma kuka , inda ta bare d'an karamin Bakin nata kamar wata k'aramar yarinya tana kuka,haka take sakin kukan Mai had'e da shagwab'a.Dr Ammar Dake kallon ta cikin tausayin ta da Mamakin lamarin nata ganin murmushin ya gushe lokaci d'aya sai Kuma kukan da ta fara Wanda duk da yake ba Mai sauti ba ne,Amma haka yake Jin sa har tsakiyar kan sa inda Kuma take zuciyarsa ta fara bugawa yadda take kukan kamar tana tafiya da zuciyarsa ne yadda kukan ke ratsa shi,Bai ce mata k'ala ba ko ya rarrashe ta sai ma Lumshe idanun sa da yayi Jin yadda suka Kara yimasa nauyi. Itama bata Wani damu ba Wanda ita kanta bata San ko kukan mene ne takeyi ba in aka tambaye ta.Ganin ya zuba mata manyan idanun nasa har baya son k'yaftawa kamar an mintseleta ko ta tashi da sauri tana sauko da k'afafun ta daga kan gadon tare da share hawayen ta da suka kasa tsayawa tana tsayar da kukan cak. Dai daituwar tsayin nata Gaban sane ya bata damar rik'e k'ugun ta cikin

Detail lengkap
WpActionLinkPanduan Muatan