"Ina son ka Amaan. Na dauki alkawarin ci gaba da kula da kai duk rintsi duk wuya. Zan ba ka gata, zan kaunace ka fiye da yadda nake kaunar kaina, sai dai...!"
Numfashi ta ja tana furzar da iska daga bakinta, "Sai dai a boye zan so ka, ba na so kowa ya san da zaman ka, kar ka rinka fitowa a kalle min kai, ina gudun kada idanuwa su yawata a kanka, bak'in idon da tsoro da kokarin ture abin da bai zama jinsi a gare shi ba. Ba na son abin da zai karce kyakkywan jikinka, balle ya had'a da zama silar kashe min kai!"
Aafiyah 'yar shekara shida zuwa bakwai a duniya ke magana da wani matsakaicin bak'in kumurci, mai jajayen idanuwa, fatar jikinshi kalar k'asa.
Macijin sai fasa kai yake, yana fitar da harshensa da mayar da shi, launin idanuwansa sun sauya zuwa jajaye, yana yi yana kad'a kanshi.
Shin a wace duniya ce muke? Ina ne za ta kai mu? Ta yaya aka yi yarinya k'arama ke magana da maciji ba tare da tsoro ba? Tabbas kowa ka gani a duniya akwai dalilin wanzuwarsa akwai kuma manufar alakantuwa da zama sila na bayyanarsa. Sai dai silar da ke cikin tafiya WATA DUNIYAR kan iya shafe labaran da aka shekara sittin ana rubuta shi.
Ku shigo ciki a yi tare da ku...kar ku bari labarin WATA DUNIYA ya wuce ku.