This is Iman telling you her story.
It is a refreshing story of love and happy-ever-after with some struggle in-between.
Labarin Maigidana labari ne da ya zamo kundin tarihin rayuwata. Ni Iman na tashi cikin soyayyar iyayena da yanuwana. Ban san damuwa ba sai da zuciyata ta gamu da wata aba wai ita SOYAYYA.
A dalilin soyayya na dandani rayuwar farin ciki da ta bakin ciki. A dalilin soyayya na koyi sanin ciwon kaina, da sanin darajar iyaye, da kuma fahimtar matsayin ďa namiji a rayuwar 'ya mace.
Ki biyo ni ku ji labarin rayuwata don ya nishadantar da ku, ya baku tausayi, kuma ya zamo darasi gareku.
Da fatan labarin zai isar maku da sakon daya ke dauke da shi a yayin da kuke jin dadin sauraren shi.
Salam alaikum.
Taku,
Aisha Humaira