Wannan muƙalace da na rubuta ta dalilin yadda wasu ke kallon Genotype test a matsayin ƙarya ko yahudanci. Ina mamakin mutumin da ya yarda da halaccin gwajin HIV kafin aure kuma yazo yana ƙalubalantar GENOTYPE TEST (Gwajin ƙwayoyin sikila). Ohhhh! Na gane. Ashe saboda gudun kar lafiyarshi ta salwantane shiyasa ya yarda HIV TEST ya halatta 🙄 Akwai wani da na taɓa gani yana tada jijiyar wuya wai a dole GENOTYPE TEST yahudawane suka ƙirƙioshi don cimma wata manufarsu, harda cewa wai bashida asali a zamanin Manzo (S.A.W), ai Sahabbai basu yishi ba, don haka yahudancine. A lokacin nace masa "Shi gwajin HIV daka yarda da halccinsa kafin aure ka gaya min a zamanin Manzo (S.A.W) sahabbai nawane suka yishi kafin aure?". Na tabbata da cewa akayi ciwon SIKILA contagious disease ne; ace in aka samu GENOTYPE mismatch uban shi zai kamu da cutar sikilar da tuni ɗaukacin mutanenmu sun yarda da halaccinsa. Amma dayake sun san ba tasu lafiyarce zata shiga wani hali ba sai kaga suna gardama. ©Aliyu Umar M. GumelAll Rights Reserved