Littafin Hisnul Muslim, Addi'o'i da suka dace da Sunnar Annabi. FALALAR ZIKIRI Allah Madaukakin Sarki ya ce: Fazkuriniy Azkurkum Washkuruliy Wala Takfuruni. Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" [Bakara, aya ta 152]. Ya'ayyuhallazina Amanuzkurullaha Zikran Kathiran. Ya ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa". (Ahzab aya ta 41). Wazzakirinallaha Kathiyran Wazzakirati A'addanlahu Lahum magfiratan Wa'ajran Aziyman. Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambatonsa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma". [Ahzab, aya ta 35] Wazkurrabbaka Fiy Nafsika Tadarru'an Wakhiyfatan waduwanaljahri Minal kawli Bil'guduwi Wal'asali Walatakun Minalgafiliyna. Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai kankan da kai da tsoro, ba da daukaka murya ba (saka-tsaki) tsakanin asirtawa, da bayyanawa, da safe da marece, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu". [A'araf, aya ta 205]. Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye da matacce ne". (Duba Sahihul Bukhari tare da Sharhinsa Fat'hul Bari (11/208). Muslim ya rawaito shi da lafazin; 'Misalin gida da ake ambaton Allah a cikinsa, da wanda ba a ambaton Allah a cikinsa kamar misalin rayayye ne da matacce". (1/539).) Kuma ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Srkin da yake mallakar ku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku daga ciyar da zinariya da azurfa kuma mafi alheri gare ku da ku hadu da abokan gabanku ku rika dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? Suka ce ka ba mu labari. Ya ce: Ambaton Allah Madaukaki". (Tirmizi (5/459), da Ibn Majah (2/1245). Duba Sahih Ibn Majah (2/316). Da Sahihul Tirmizi (3/139).)
85 parts