🎀 *ILHAAM*🎀
BY
Sadeeyah A maru {Sadeeey}
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin ga mahaifiyata,abun alfaharina, Allah ubangiji ya jikanki ya gafar ta miki yakai haske kabarinki.🤲🤲🤲
Page 01
Tafara nisa cikin gyangyad'in data fara wanda haryakai
mafarkan bazata sunfara ziyartar k'wak'alwarta, batare da zato ko tsammaniba taji saukar ruwa mai sanyin gaske yana ratsa sassan jikinta.
Sanyinne ya ratsa ilahirin jikinta wanda yai sanadiyara farkawarta cike fargaba, tsoro da razani duka lokaci guda suka dirar mata, ba komai ya haddasamata hakan ba sedan sanin cewa INNA ce mai mata wannan aika-aikar.
Kuka tafashe dashi wanda yai sanadiyar k'aruwar 6acin ran Inna haryakai ga tad'aka mata duka tare da cemata....
"Munafukar yarinya! Yanzu tadakin da nayi donki tafi d'ibamin ruwa ashe baccin naki na asara kikacigaba anan?, Lallai kin isa kuma jikinki seya gayamiki"
Inna ta fad'i haka tare dasa k'afa tabuge ILHAM sannan tawuce tana bambami.
Tana kuka tare da rawar d'ari haka tanufi inda tulun d'iban ruwanta yake ta d'auka sannan ta nufi rafi.....
Ahanya bata had'u da kowa ba saboda lokacin yawancin al'ummah suna gida suna bacci wasuma suna kaiwa ubangijin halittu kukansu kasancewar gari baigama wayeba.
Tana tafiya tanashan wahala haka harta isa rafin, kasancewar sunada tazara sosai da rafin amma hakan baisa Inna najin tausayinta ba, watannin baya dasuka wuce wani mai kud'i yashigo garinnasu tare dasawa akajawo musu ruwa kusa dasu, amma saboda son irinna Inna tace batason ruwan dake fitowa daga k'arfe na rafi takeso.....
Idan naga comments mai yawa sai mun hadu a next page.
Sady🎀