Me Mahaukaciyar da bata um bata um-um tayi? Laifin wani baya shafar wani, saboda haka Banga aibu acikin auranta da Emanuel ba, dan haka ni Malam Adamu zan damƙata a hannun Emanuel matsayin matarsa a sati me zagayowa.
Zai fi kyau ki adana wannan hawayen naki domin akwai ranar da zaki buƙacesu suƙi zuwa, ranar da zaki san SIRRIN ƁOYE* wanda sanadinsa za kiyi kukan jinin dani na jima da yinsa a baya, akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanina dake Merry, sai dai ba zan sanar dake ba, ba kuma zan sakeki ba har sai ranar da naga hawayen nadama na zuba daga idon wadda ta kawoni duniya lokacin data faimci wacece KE wanene kuma NI.