Zan shiga gidan na jiyo muryar Iro na cewa "A dai dinga jin tsoron Allah." Murmushi na yi na Juyowa na kalleshi cikin fuskar rashin mutumci, na ce "To da tsoron wani k'aton banza irinka zan ji?." Ina fad'in hakan na shige cikin gida. Armiya'u ya kalle iro ya ce "Amma dan Allah Baabaa baka ji kunya ba?." Kallonshi ya yi sama da k'asa, ya ce "Kunyar me zan ji?, abin da muka saba ni da ku.!" Dukansu suka had'a baki suka ce "Muka dai koya a wajenka." Sule ya ce "Gaskiya Iro ka tsaya ka ma kanka karatun ta natsu, kai ko kunya ma baka ji yarinyar da bata wuce 18 to 19 years ba, ta raina haka? bayan d'an banzan dukan da ta maka a wancen lokacin? Ni fa gaskiya na fara saduda da wannan rayuwar fa, munafurcin nan dai tunda ba ibada ba ne wlhy ajiye shi zan yi gefe na kama dahir.!" Iro ya ce "Kai ne munafuki daman a wajen nan, ka ga idan ka ajiye shi ka taimaki kanka da 'yan k'annenka.!" A zafafe ya ce "Kai Iro idan ana maganar babban munafuki a wajen nan, kai ka ma isa ka saka bakinka?." Cikin fad'a Iro ya ce "A'a ba zan saka ba tunda ina tsoronka.!"
110 parts