*BAK'AR MASARAUTA* *Hausawa kan ce 'Ana bikin duniya ake na k'iyama, lokacin da wani yake kuka, wani dariya yake, kamar misalin yadda Uwa ke d'aukan ciki ta raine shi da wahalhalu kala-kala, tayi burin ta haife cikin domin ba wa jariri ko jaririyar duk wata kulawa da za su samar da tagomashin tarbiyya da kyawawan d'abi'u ga abin da ta haifa, ku hasaso yadda wannan uwa bayan duk ta gama wad'annan wahalhalun za ta tsinci kanta a bak'in yanayin da za a raba ta da abin da ta haifa ta hanyar zalunci, a yayin da ko cibi ba a yanke masa ba, shin da me za ku kwatanta?* *Tana da k'arfin ikon da kwarjininta kad'ai kan girgiza jama'ar da take mulka har su kasa nutsa idanuwansu cikin nata, shi kad'ai ya yi zarrar da yake ji ya isa jera kafad'a da ita, shin me ya taka ne duk da kasancewar sa bawa?* *Mata na rububin kasancewa da shi duk da bak'ak'en d'abi'un da suka yi wa rayuwarsa k'awanya, izza da guguwar mulki ta taka muhimmiyar rawa wurin kasancewarsa haka* *Da shi take kwana da shi take tashi! Tamkar Sallar farilla haka mafarkinsa ya zame mata wajibi a duk daren duniya, ta yi namijin k'ok'ari wurin gano shi amma sai dai kash....* *SABON SALO NE MAI GIRGIZA ZUKATAN MASU KARATU, DUK A CIKIN LABARIN BAK'AR MASARAUTA. KARKU SAKE A BAKU LABARI.