*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi rayuwar wasu masoya guda biyu wanda dukkan iyaye da yan uwa sun san wannan soyayyar, sai dai me? MARYAM ta yi rashin HAIDAR a daidai lokacin da zuciyarta ke tsananin kaunarshi, a daidai lokacin da tafi kaunar sa, a dai dai lokacin da take zaton ba abinda zai raba su, a lokacin da take tunanin burin ta ya gama cika a rayuwar ta gaba daya. Daga nan rayuwar ta ta fada kunci da tashin hankali, wanda ta dalili haka ta rasa maganar ta bama wannan ba wata daya da rashin HAIDAR aka gano MARYAM dauke da cikin a dalilin cikin mahaifin ta ya kore ta daga gida wanda barin ta gida ke da wuya ta manta wacece ita, ta manta kowa nata. #To wai wannan cikin wanene? #Me ya faru da HAIDAR (Mutuwa yayi ko kuwa)? #Me zai faru da rayuwar MARYAM?