Gidan gandu,haka kowa ke kiran gidan mu saboda yawan iyalan gidan tun daga kan iyaye da kakanni zuwa kan yaya duk muna zaune ne acikin gidan gandu.
saidai abu daya shine, duk wani kalar hali da kake nema inkazo gidanmu to ka samu ,kama daga shaye shaye ,dabanci sata,koma dai menene,abinda zai baka mamaki shine duk iskancin mutum a gidan hatta dabbobin gidan suna shayin rashin mutuncina tun daga kan iyaye kuwa har yayansu babu wanda hantar cikinsa bata kadawa idan yasan ya shiga gonata ,nice nan SAMEEMAH!!!!...................Tofahh.
Bazan iya ba Abdul! Bazan iya neman taimakon mutumin da ya aureni kawai sbd na mare Shiba.
Bazan iya neman taimakon mutumin da kullum burinsa ya d'auki fansa akaina ba.
Kawai dae ina neman taimako a gurin ubangiji na sbd nasan komai yake faruwa *DA SANIN ALLAH* domin baya barci kuma rahamarsa me isa ce ga kowa.