Shekaru goma sha biyu! Shekaru huɗu a cikin sha biyun nan sunyi sune cikin soyayyar da bata hango rabuwa a cikinta ba, sai kaddara ta gifta. Ta shiga tsakaninsu na shekaru takwas, shekarun da ta yanke tsammani a cikinsu, shekarun da abubuwa da yawa sun faru a cikinsu, ashe kaddara bata gama dasu ba, sai ta dauketa ta sake jefawa rayuwarshi. Me ya faru a tsawon lokacin nan? Me kuma zai faru? Tunda daman ai hausawa sunce KOWA YA DAKA TA BADO... Yasmeen ML
More details