12 parts Complete _Duniya makaranta a lokacin da wasu suke shiganta a lokacin ne wasu ke barinta,wasu na zuwa Duniya wasu kuma na barin Duniya, Rayuwa kamar shafin littafi ce,baka sanin abinda yake bangwan baya dole saika buɗe shafin gaba,muna zuwa Duniya ne ba tare da sanin abinda ke cikinta ba,wasu na zuwa a makance, wasu a kurmance,wasu kuma babu ido,kunan jin magana,uwa uba wasu basa zuwa da ƙafar takawa_
_Nakasa bata taɓa zama kasawa,haka kuma ƙaddarar data mai dashi nakashasshen zata iya sauya, kullum cikin zullumi yake, shin tayaya ne rayuwa zata kasance masa? tayaya yana nakashasshen zai iya mulkan dubban jama'a? Cikin ana tsangwamarsa bare ace ya zama shugaba,yaya jama'ar gari zasu ɗauke sa?tayaya zai gabatar da mulkin bayan Allah ya taushe ta hanyarsa rasa wani ɓangare na jikinsa?_
_Zuciya nada abubuwan ban mamaki,abinda kake so ita bashi take so ba,kullum yana ganin abin kamar mafarki amma yadda abin ke zamar masa a gaske shike masa mamaki,me zaiyi wanda zai samu farin ciki?me zaifi wanda zuciyarsa zata daina kewa ta daina ƙunci,duhun dake cikinta haske ya mamaye shi, FARAUTA shine abinda zuciyarsa ta yanke masa,abin mamaki shine tayaya nakashasshe zai iya zama mafarauci? Tayaya farauta zata masa maganin damuwarsa?.._
'''SHIN ZAI IYA KO A'A?
YANA CIN RIBA A FARAUTAR KO A'A?
KUNA TUNANIN WATA RANA NAKASAR SA ZATA IYA ZAMA RIBA GARESA?