BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
MA'U 1
Ina zaune can kur'yan daki na na hada kai da gwiwa cike da damu , ni dai ba kuka nake yi ba , sannan ban san mai zan kura kai na a lokacin ba , mutum mutumi ko mutum mai rai , a can gefe kuma ma'u ce take shishshikan kuka , a hankali ta matso kusa dani ta kama hannu na , cike da damuwa tace umma muna don Allah ki yafe min wlh ni fa bana son mal , kuma wlh idan aka matsamin kashe kaina zanyi ko na gudu , duk da cewa dakin babu ishashshen haske amma acikin idon ta na hango zata iya aikata abinda ta fada .
MA'U 2
Da sauri na maida hankali gare ta , cikin jin dacin ta nace a kul din ki ma'u kar na sake jin kin furta irin wannan maganar , bana son ki zama mara biyayya wa mal , koba komai yayi miki komai a rayuwa , ma'u ta kara fashewa da kuka , hawaye wani na bin wani a jajayen idanun ta da suka kada suka yi ja kamar garwashin wuta , magana take yi cikin kuka tun tana fada a hankali har na fara gane mai take cewa , na shiga uku ni ma'u mai yasa duniya za tayi min haka , mai yasa na zama daya daga cikin mutane mara sa sa'a a rayuwa .
MA'U 3
Haka kawai an raba ni da abin sona , an hadani da wanda yayi jika dani , an sani cin amanar uwata wadda ta soni tamkar yar da ta haifa ,wlh bazan taba yafewa duk wanda yake da hannu acikin wannan zalincin da akayi min ba , sai Allah ya saka min , umma muna ta kwashe ta mari jikake tas tas , baki da hankali ne ma'u iyayen naki kike jawa Allah ya isa , Allah sarki ma'u mai makon taji haushin dukan da nayi mata sai ma ta kara makalkale ni tana umma ta don Allah ki cece ni , ki dauke ni daga gidan nan dama bani da wani gata sai ke .