Aure!!! Idan aure ya mutu a ƙasar Hausa, ba wanda yake cutuwa sama da mace. Amma al'umma ita za su zarga a ce ta ƙi zaman aure. Haka idan rashin lafiya ta faru a zaman auren. Tamkar al'umma suna mantawa zaman aure na mutum biyu ne. Duk yadda ɗayan ya so a zauna, ɗayan kuma ba ya so ai abun kamar da wuya a samu biyan bukata.