We've updated our Content Guidelines.
Review the latest guidelines to keep sharing stories safely.
SANADIN BESTY

SANADIN BESTY

  • WpView
    Reads 650
  • WpVote
    Votes 23
  • WpPart
    Parts 14
WpMetadataReadOngoing1h 55m
WpMetadataNoticeLast published Wed, Jan 4, 2023
WpInfo
Non-Fiction
Tagsrubby
Zama da wan da ku ka mayar da juna besty zama ne na amana, soyayya, tausayi da kuma tsan_tsar kulawa ta hakiƙa wadda akasarin wanda kuke soyayya ba lallai bane a samu irin wannan kulawar daga gare shi, besty ne mai tsayawa ya fahimci damuwar da ake ciki har ya yi ƙoƙarin magance ta ko ya bada shawarwari. Besty abokin rayuwa na, yadda na dauƙi besty da muhimmanci shi ne silar rushewar farin ciki na, Besty ya taka muhimmiyar rawa a labarin Rayuwa ta, ta ko wanne bang'are, ba komai bane ya ja min sai bashi wata ragama a cikin rayuwa ta, inda yake ja tamkar doƙi da akala.... Kaii bari in takaice muku besty shine silar rabuwar mu da YA NOOR !!! Besty farin cikin soyayya Besty ɓaƙin cikin soyayya.. Besty shugaba kuma jagaban raba masoya ta hanya mai sauƙi. Ka!! kai!! kai!!! lamarin na besty fa sai dai kawai ku biyo alkalamin RUBBY dan jin labarin Ni RAUDAH da Bestynah DEEN da mu ka kasance besty ga junan mu... Mene ne karshen alakar ta mu? Amsar na cikin littafin SANADIN BESTY Gajeren labari ne (short story) Doƙoƙin shiga wannan gidan
All Rights Reserved
#8
rubby
WpChevronRight
Join the largest storytelling communityGet personalized story recommendations, save your favourites to your library, and comment and vote to grow your community.
Illustration

You may also like

  • SAWUN GIWA...!🐘
  • SAFEENATU
  • SHAREEF 2023
  • NANATOOU (DIYAR KAKA)
  • KAICO NAH
  • AURE UKU(completed)
  • BAKAR WASIKA
  • MAI ƊAKI...!
  • TAFIYAR MU (Completed)
  • KWANTAN ƁAUNA

"Dallah gafara can malama, har ke kin isa ki mana abunda Allah bai mana shi ba? Akanki ne aka Fara irin hakan? Ko kuwa akanki ne za'a daina? Sai wani ciccika bak'in banza kike awurin kamar zaki iya tabuka abun kirki idan har mukayo gaba da gabanta, Ke kin sani sarai ba yabon kai ba ammh wallahi tsab zan tumurmusheki anan wurin kuma in zauna lfy lau agidan Mijina, Kuma ki saurareni dak'yau, halinki ne ya jaza miki wannan cin amanar, Ke kowacce mace tana mafarkin samun miji kamar naki ammh ke Allah ya baki salihin mutum mai tsoron Allah, Sai ke kuma kikai amfani da hakan kina muzguna masa? Bashi da iko da gidansa sai yadda kikai? Babu wata muryar da yake tsoro da shakka face naki? To wallahi ki sani da'ace ayau bani da aure ne to Kinji nace Allah mijinki zan aura, zan shawo kansa kuma dole ya saurareni don kowacce mace da salon nata kissar, balle ma idan yaga ina masa abunda ke baki masa shi, kin san Zuciya nason mai faranta mata, ke mahaukaci kankat kenan yana kaunar mai faranta masa balle mai hankali, Hajiya Sa'a kiyi kuka da kanki ba dani ba don iya allonki ne yaja miki Faruwar hakan." Kuka sosai Hajiya Sa'a ke rerawa don ta kasa Furta komai kuma, Hajiya Aisha ta gama kashe mata jiki, Kama baki Hajiya Aishar tayi tana Fadin"Ai baki ma soma kukan ba, nan gaba kadan zakiyi wanda yafi wannan, kuma ki saurareni dak'yau, ga 'yata nan amana, Ku Zauna lfy ke da ita don wallahi kika sake naji ance ko ciwon kai kin sakata Allah saina lahira ya fiki jindadi, don kwarai zan cire kunyar Surukuta da amintar dake tsakaninmu musa wando kafa daya dani dake, Sabida haka ki kiyaye sannan Kuma akyalesu su sha amarcinsu Cikin kwanciyar hankali, don wallahi Hajiya Sa'a tashin hankalinsu kema tashin hankalinki, Tun wuri ki iya takunki don karki ce ban fada miki ba, Suhaila ita kadai ce 'yar da Allah ya bani sabida haka zan iya yin komai akanta, Ki huta lfy."

More details
WpActionLinkContent Guidelines