A yanzun maza da yawa suna shunning daga responsibilities dinsu, kamar yadda mahaifina ya auri mahaifiyata ya barta take daukar dawainiyar mu. Idan ya dawo ta samu ciki se ya tafi yayi shekara biyar Bai dawo ba, mu din mun tashi a hannun mahaifiyar mu, ita din ce komai namu, cinmu, shanmu da Kuma suturar mu. Sunana Unaisa wadda akeyiwa take da gayun duniya, ni din Yar gayu ce Kuma kyakyawa me ilimi.....