Ta kasance budurwa mai matsakaicin shekaru, a dalilin so ta ɗauki kasadar da har ta mutu ba zata taɓa daina dana sani ba.
Bata taɓa aure ba, bata taɓa zina ba, ba kuma a taɓa yi mata fyaɗe ba, amma ta ɗauki ciki.
Duk wani buri da take son cikawa ta cika, sai buri guda ɗaya ne ya zame mata cikas, wannan dalilin ne ya ruguza mata dukkan wani tanadi da tana yi ga rayuwarta.
Wane buri ne? Wacece? Ta wace hanya ta samu cikin? Masu karatu ku biyoni a littafin nan domin warware komai.