Wacece ni labari ne akan matashiyar da ta taso cikin wata irin rayuwa mai ďaure kai da jan hankali. Ba abun mamaki bane idan kishiyar mahaifiyar mutum ta tsane shi amma mahaifiyar kanta ta nunawa ďanta tsantsar tsana da tsangwama da kyara abun ban mamakin gaske ne! Ko wani dalili yana sa uwa ta tsani ýarta? Wanne dalili ne wannan da zai iya juya matsananciyar soyayyar da uwa ta ke yi wa ýarta ta koma kiyayya zalla? Ita kuma ýar wacce irin rayuwa zata yi? Wanne irin kalubale zata fuskanta? Wanne irin hali zata shiga kuma ya za'ai ta warware wannan kullin? Wa zai bata amsar wannan tambayar mai nauyi? Shin yaya aka dauki matsalar fyade a kasar Hausa? Wanne irin hukunci ake yankewa wanda yayi da wanda akai wa? Ya rayuwar macen da wannan kaddarar ta faruwa da ita take kasancewa kuma wanne irin trauma take shiga? Wanne irin effect abun yake haifarwa a gare ta mentally and physically? Wacce hanyar ya kamata abi domin a warwaware wannan matsala mai cin tuwo a kwarya?All Rights Reserved