Kuka haɗe da dariya ne suke ta shi a cikin dajin, zuwa can ta hango inuwar wata hallita na tunkaro ta, matsananciyar guguwa ce ke tashi bishiyoyi na kaɗawa da ƙarfa yanda kasan za su jijjigo daga jikin jijiyoyinsu.
Cikin wani irin gwamamman yare ta riski muryar inuwar tana cewa, "Sai kin halaka ke da abin da yake cikinki, kin zama halakakkiya keda tsiron da ke cikinki." Ba ta yi aune ba ta fara jin abu na bin ƙafarta zuu! A daidai lokacin da ta ji wani irin nishi ya taso mata.
Durƙushewa ta yi a wurin tana murƙususu, nan take wani irin kukan Jarirai mai haɗe da kukan Jaki ya fara karaɗe lungu da saƙon da ke cikin dajin tamkar zai tsage gida biyu. Sannu a hankali Jarirai suka fara rarrafowa suna zageta kamar ana zagaye wainar gero. Duk da halin da take ciki bai hanata yunƙurin tashi domin tseratar da rayuwarta ba, amma ina! Haihuwa ta tunkarota gadan-gadan nan take jaririn ya faɗo.
Sannu a hankali ya rinƙa bin duk wurin da jini ya zuba yana lasa shi da sauran 'yan uwansa Jarirai, tamkar waɗanɗa suke da'irar ƙungiyar asiri. Raihan da ke durƙushe da sauri ta zabura kamar wacce aka ɗanawa ruwan dalma, tana yunƙurin tashi nan take mabiyiya ta faɗo. Kamar yanda Kura take ƙishirwar nama haka suka afkawa Mabiyyar kafin wani lokaci tuni suka gama da ita.