"Ita ce ta hannun dama ta. Bazan taɓa bari wani abu ya cutar da ita a gaban ido na ba. Haƙiƙa Maryam ta wuce aminiya a wajena, ta zame min ƴar uwa! Ta nuna min halacci a lokacin da nake cikin jarabawa, ta kuma ƙaunace ni a lokacin da ƙawaye suka guje ni. Kai Maryam ta zame min sutura a lokacin da ake ƙoƙarin yaye ni duniya tayi min dariya. Haƙiƙa bana shakkar zan iya rasa raina domin ceto rayuwar ta".
Sai dai a yayin da Amira ta ɗau wannan alwashin ta haɗu da barazana me rikitarwa ga cikas ta warare da dama. Shin ko zata gajiya wajen cika wannan alkawarin nata?
***
Labarin Ina mafita ƙagaggen labari ne domin ya nishadantar kuma ya ilimanrar ya kayatar da ku.