Bai karasa sauran maganar dake bakinsa ba suka ji magana a bayansu "ke Faheema!..." Cikin sauri Faheema ta ware jikinta da nashi ta waigo tana duban mommnta dake saukowa saman matakala tana dubansu cike da ayar tambaya a kwayar idanunta, shima Ammar duban yayar tasa yake yana lumshe idanunsa a hankali, hankali a tashe Hibba ke kallonsu "Me nake gani haka, Faheema what are you doing?" Cikin i'ina ta soma fa'din "uhm..mommy, ina yiwa Uncle Ammar sannu da zuwa ne" "Kina masa sannu da zuwa shine kike shigewa jikinsa kika mance da kanki haka?" Faheema tayi shiru tana dubanta don bata fahimce inda ta dosa ba, this is not the first time da take hugging Uncle Ammar, why is this different? "Baki san kin girma ba yanzu Faheema? Da da yanzu ba da'ya bane, You're no longer a little girl" "But mommy...uncle Ammar ne fa" "Ko ba Uncle Ammar din ba" Hibba ta bata ansa ta juyo tana duban Ammar din dayayi shiru yana dubansu... Although this is a spin-off of "QALBINA KECE ZAKI FIDDANI" you don't have to read the first book to understand this story. (I'll advice you to read the first book tho)😄 This book is also a stand alone. Wanan cigaban labari ne akan Faheema da kuma kawunta Ammar, Ammar ya jima yana dawainiya da son yarinyar yayarsa, bai ta'ba jin son wata ya mace a ransa kamar yanda yake jin Faheema ba, sai dai yanzu ya zaiyi da circumstances? Will he be able to let go of these feelings he has for her? Shin yayar tasa zata amince ta bashi yar'ta ko yaya Ku biyo kuji yanda labarin zata kasance...🔥