Najib anya kai mutum ne? Anya da zuciya a k'irjin ka? Najib Nabila ta soka a lokacin da en mata suke gudun ka ciki har da y'an uwan ka, Nabila ta aure ka a lokacin da ko wacce mace take cewa baza ta zauna da MAKAHO ba, Nabila y'ar gata ce gaba da baya amma ta amince ta zauna da kai, y'an uwan ta gabad'aya basa san auren ka da ita amma ta zab'i ta b'ata da kowa dan ta kasance da kai, gidan nan da kake ciki nata ne ta baka kyauta cikin kadarorin da Allah yayi mata tace ka rik'e kar kuma ka fad'awa kowa nata ne, ta sadaukar da aikin ta sabida kula da kai, ta sadaukar da kud'in ta mak'udai ta fitar dakai k'asar waje aka gyara maka idon ka ka dawo kamar kowa bayan kashe kud'in da tayi kafin aje Germany, shekaru sama da ashirin kana a haka cikin zaman ku na shekara d'aya ta dawo dakai mutum kamar kowa, duk da wannan tarin alkhairan ta gare ka yau kaine da bakin ka kake cewa baka santa ka tsane ta? Najib Nabila ce fa? Nabila fa Najib, yarinyar y'ar shekara 22 kacal kake so ka jefa rayuwar ta cikin tashin hankali sabida san zuciyar ka, Najib anya kai mutum ne?".
Tirk'ashi! Ku kasance da labarin MAKAHO NE dan jin yadda zata kaya.