Ledar kazarta ta nuna masa tana maƙale hannu ta ce, "Kazar nan ce take cizo na a hannu, kuma ni ka zo ka kwanta a nan." Da mamaki Khalid ya furta, "Kaza kuma? Gasasshiyar kazar ce take cizonki..." Khalid bai rufe baki ba ya ji ledar kazar ta bada ƙaraas alamun taunar ƙashi, da sauri Khalid ya sake buɗe wa sai dai ga mamakinsa yana buɗe ledar ya ga sai taunannun ƙashi, wasu ma an yi dugu-dugu da shi. Cinyoyin kazar ne kawai aka cinye tsokokin ba tare da an tauye ƙashin ba. Yana shirin yin magana ya ji Walida ta saki ƙatuwar gyatsa sannan ta ce, "Uncle zan sha ruwa." Khalid ya ƙwalalo ido waje ya ce, "Ina kazar cikin ledar?" Walida ta ce, "To ai sai na sha ruwa zan ci." Khalid ya sake bankaɗe ledar ya ce, "Ba yanzu na nuna buɗe kazar har kika ce ba gashin inji ba ce?" Walida ta sake sakin gatsa haɗe da ɗaukan tsinken sakace tana kwakwule haƙoranta.