32 parts Complete DR UMAIMAH USMAN BULAMA,Mace yar kimanin shekara ishirin da tara ,
Babbar surgeon A asibitin CITY TEACHING HOSPITAL ,
Aure Uku, Ζ΄aΖ΄anta uku .
Mace mara san hayaniya wadda tasan kan Aikinta ,babu abunda tasa a gabanta illa bawa Aikinta babban muhimmanci kana yaranta wadda kaΙdarar samunsu ta rarraba mata Aure .
Kalma Ιaya zaka faΙa ta bata mata rai shine kushe mata Aikinta ko nuna wasa a duk wani abu da ya shafi Aikinta .
Ita Ιin kwarariyace kuma gogaggiya akan duk wani abu da ya safi surgery,ba kasar ta ba hatta a wasu kasashen tana zuwa aiki.
Bangaren soyayya fa?
Bata dauki soyayya a bakin komai ba tunda dukkan Aurenta guda Ιaya ne tayi na soyayya kuma shima bai karbe ta ba wanda hakan yasa ta yanke shawarar saka soyayya a Ζwandan shara duk da kuwa tayin da ake kawo mata ,ta gama yanke imani da soyayya akan duk wani Ιa namiji wanda haka yasa mutane da dama ke mata kazafi da mata take so duba da Ζin mazanta karara a fili.
Amma menene dalilin tsanar tasu da tayi?
Menene yasa ta cire mazan daga tunaninta da zuciyarta baki daya?
Shin zata faΙa soyayyar wani Ιa namiji ko a'a?
Idan zata faΙa wanenen wannan mai sa'ar?.
DR IMAM MUKTAR PAKI,
Saurayi dan kimanin shekaru Ishirin da tara ,bai taba Aure ba,
Dalibi wanda yake neman sake gogewa akan Aikin surgery ,shekara Ιaya wadda kareta ne kaΙai zai bashi kwali da kuma lasisin Fara yin surgery ,kaddara itace tayi aikinta ta Ιauko sa kan kachakar ta kawosa CITY TEACHING HOSPITAL inda yake Ζarkashin jagorancin likitar da kowa ke tsoro da shakka,
Mene zai faru idan shi bai ji wannan feelings Ιin ba sai wani daban wanda shi kansa bazaya iya fassarawa ba?
Shin ya wannan kaΙdarar tasu zata kasance?
Shin Wanne irin chakwakiya Imam ke shirin Ιaukowa kansa domin wannan likitar da ya ke kan giyar so AURENTA UKU ,Ζ³aΖ΄anta uku a yayin da shi ko na fari bai taba yi ba.
Ku biyo Ιiya jamilu domin jin yarda wannan labarin na IMAM da UMAIMAH zai kasance !