41 parts Complete Mature#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017
#2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017
#3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017
#4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017
Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu.
Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci.
Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo ja baya a cikin al'umma.
Rauninta ya sa aka yi amfani da wannan damar wajen muzguna ma ta!
Rauninta ya zama katanga a gare ta wajen samuwar ilimi.
Kasancewarta MACE! Na iya sa wa ta zamo MADUBI a cikin al'ummarta,ta zama a bar kallo, a bar koyi.
Cin zali da keta haddin mace wannan ya taka ma dokar addini.
Addini be ware ta ba wajen neman ilimi. Haka ma a sauran bangarori na rayuwa.
Haka Halimatu Ammah ta taso cikin bahaguwar rayuwa mai cike da qalubale.
Shigowar zaratan matasa da suka taka rawar gani a rayuwarta ya zamo ruðani a gare ta. Kowannensu ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin ci gabanta.
Hakan yasa ta kasa tantance wanane zabinta tsakanin MUKHTAR da ARK a karo na biyu da za ta fada rayuwar aure. Wacce take dar-dar da ita, a sakamakon TUNA BAYA na rayuwarta da SALISU.
Ku biyo ni dan jin tarin amsoshinku.
Ayeesh Chuchu