Talaka mutum ne mai zafin rai, son kai, rashin tawakkali da kuma rashin godiyar Allah, ban ce ko wane talaka haka yake ba, amma ni a haka nake kallonsu domin na tabbatar da haka ne a lokacin da zanen ƙaddarata ya canza daga fari zuwa baƙi, kuma na tabbatar da hakan ne a lokacin da allon fahimtata ya kalli Alhaji Ma'aruf da Naufal da kuma ni kaina.
Ita soyayya wata aba ce da kan ruguza tanadin shekaru ɗari a rana ɗaya ko yini ɗaya koma ince minti ɗaya, kamar yadda ni tawa soyayya ta min sanadin rashin gani da kuma rashin ji sannan babu wani ɗan jagora...!
A yayin da nake kallon masoya a matsayi ƴan wahala, kuma wanda basu san inda ke masu ciwo ba, a lokacin ne littafin ƙaddarata ya buɗe min mummunan shafi, bana soyayya ba kuma na sha'awarta sai gashi na zama nakasashshiya a sanadin so, na rasa gane shin ɗaukar fansa ne ko alhakine ko kuma zanen ƙaddarata ne a haka?