Ba Ni Da Laifi! Kaddara tana zuwa maka a yadda baka tunani, Kuma a matsayin mutum na musulmi Dole ne ya karba wannan kaddarar. Ko kunsan meye tawa kaddarar?
Hannuna na rawa na karba takaddun da Dadaa yake Miko min, Ina karba cikin sauri na bude envelope din, a take naga takaddu da yawa, sunan Zayyad Abdulhamid ne a jiki, a take gabana ya fadi, nayi saurin scanning cikin paper da idanuna da suka firfito kamar zasu fado kasa, takardar farko wadda ta kasance ta asibitin koyarwa da ke garin Lagos, ta can kasa result din genotype dinshi ne "AS" na dago hannuna na rawa nace
" Dadaa Amma ba Zayyad di na ba ko? Bashi bane AS ko? Dadaa..."
Tuni idanuna Suka fara zubar da hawayen, na tuna farkon haduwar mu, na fada Masa Ina da sickle cell disease, se yace min Yana da tabbacin jinin shi AA ne, Amma Kuma ya nake ganin akasin Haka.
" A'isha ki saurare ni!"
Nayi saurin katse shi Nima Ina fadin
" Dadaa Ina son shi, Dadaa ku Kara dubawa ba lallai wannan result din gaske bane"
To Amma me? Takaddun hannuna sun nuna result da yawa har da na AKTH, Shika, national hospital! Result din Ina nake nema Kuma? Bayan wannan hudun dukka asubutoci ne da ake ji dasu a kasar nan Baki daya. Hawaye ya cigaba da sauka min, Ina jin kamar zuciyata ana babbaka ta ne, Ina jin kamar blow din yayi min yawa!
Ba Ni Da Laifi kasancewa ta me sickler, kasancewar genotype dina SS ne! Amma bansan me yasa mutane ke gudu na ba, bansan me yasa kowa baya Sona ba, shi ma Zayyad Dana kwallafa Rai na Akan shi se jinin shi ya kasance irin Wanda bazan iya Zama dashi ba!
Labarin sabo ne! Salon ma Kuma sabo ne! Tafiyar ma Kuma sabo ce! Labarin na A'isha ne, ko Kun taba Jin labarin sadaukar wa? Ko Kun taba ganin labarin kauna da soyayya? Ni din nan ce shatuuu, ni din na rubuta Unaisa, Kuma na rubuta Mace a yau, na rubuta Afiyya da Fara Yar shehu!