Soyayyar uwa soyayya ce da ake haifar ƴaƴa da ita, musamman ma ƴaƴa mata, sedai wannan ya sha banban da rayuwar Meemerh, a duniya babu wacce ta tsana kamar mahaifiyarta, bata tashi tare da ita ba amma ko yaushe addu'ar ta da fatan ta ko a mafalki kar Allah yanuna mata ita, duk da tsangwamar da ta tashi a cikin ta na dangin uba da matansa amma bata jin tsanar su kamar yadda ta tsane mahaifiyarta..........