_*" YA SAKE NI..YA SAKE NI..Yaya Saifuddeen ya sakeni na shiga uku na..!*_ _*Take fada kafin tayi zaman yan bori saman cafet din daya malale Dakin Mami dake saman Darduma tana lazimi ta mike a Firgice gabanta na fadi Hajiya zuwaira data fara barci sama sama sai da ta tashi a Firgice gabadayansu suka yi kan Majeeda suna tambayanta me ya faru..!?*_ _*Ta kara Daga farar takardan hannunta tana fadin"Ya sake ni..yace ya sake ni..!*_ _*Sai mami ta Dafe kanta tayi baya kamar zata fadi hannayen kanwarta Zuwaira ya tareta tana fadin"Yaya zulai ki yi a hankali fa..!*_ _*Mami ta kalleta kafin tace"Na shiga uku zuwaira YARO zai kasheni kwana na bai kare ba..?*_ _*Jiya fa aka daura masa aure da Majida itama ya saketa kamar yadda ya saki Amira..?*_ _*Anya yaro na da lafiya kuwa..?*_All Rights Reserved