Alwashin da EMRAN BELLO ƘARAYE yayi akaina abu ne da hankali baze taɓa ɗauka ba, amma kasancewarsa mutum mai kafiya akan Ra'ayinsa yasa tsoro mai tsanani ya ɗarsu a Zuciyata......!
Hawayen da nake dannewa ne suka ziraro daga kwarmin idanuna, a lokacin dana tabbatar da cewa ƊAN MUTAN ƘARAYE ya gama kassara sauran nutsuwar dake zuciyata, daga baya kuma yazo ya ƙwace komai daga gareni babu abinda yay Saura..
A cikin Rayuwata bana buƙatar na ƙara tuna komai duk abinda ya danganceta, don Babu komai a cikin tunawar face ƙunci da tarin baƙin ciki. a halin da nake ciki a yanzu bai wuce in samawa kaina mafita akan CIKIN dake jikina ba.....!
Kwatsam a ɗan wannan taƙin sai gashi ƙaddara ta shigo da SARDAUNA ALIYU ADAM cikin Rayuwata, shigowar data haifar da abubuwa masu Tarin yawa.... Waƴanda sukasa na Fahimci ITA CE SANADIN baƙin cikin da ke cin zuciyata na tsahon lokaci✍️